Hakika yanzu a duniyarmu ana ganin wani sauyi na yanayi game da kekunan da ake amfani da su. A da jama'a sun fi son kekunan da ake amfani da su kan hanyoyin mota, ko kuma kananan hanyoyin da aka kebe a dab da hanyoyin mota. Amma a yanzu mutane sun fi karbar kekuna na musamman da ake iya hawansu a wurare masu duwatsu. Wadannan kekunan suna da nau'ika daban daban, sai dai yawancinsu suna da taya mai girma, da na'urar canza saurin gudun keke, gami da na'urar rage girgizar wili. Wadannan na'urori na baiwa keken damar gudu cikin duwatsu ba tare da gamuwa da matsala ba.
171109-wasan-tseren-keke-a-wutare-masu-duwatsu-bello.m4a
|