in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban Djibouti
2017-11-24 19:59:57 cri

Yau Jumma'a 24 ga wata, a nan Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Djibouti Ismail Omar Guelleh, wanda ke ziyarar aiki a kasar ta Sin.

A yayin ganawar tasu, mista Li ya nuna cewa, kasar Sin na fatan hada kai da Djibouti domin taimakawa juna, ta yadda Djibouti za ta kai ga raya tattalin arziki, da zamantakewar al'ummar kasar, da kyautata yanayin rayuwar jama'a.

Ya ce kasar Sin ta karfafa gwiwar kamfanoninta masu karfi, wajen zuba jari a Djibouti. A daya hannun Mr. Li ya yi fatan ganin Djibouti ta samar wa kamfanonin kasar Sin sauki da tsaro.

Da yake maida martani, Mr. Guelleh ya ce kasarsa ta Djibouti na fatan amfani da fifikonta, wajen zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da Sin, a kokarin samun ci gaba tare. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China