in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma nasara game da binciken FTA tsakanin Sin da Mauritius
2017-05-25 19:51:33 cri
Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce an cimma nasara game da binciken yiwuwar aiwatar da yankin ciniki cikin 'yanci tsakanin Sin da kasar Mauritius.

Ma'aikatar cinikayya ta kasar Sin ta ce binciken mai lakabin FTA, wanda aka kammala cikin nasara, an gudanar da shi ne bisa burin kasashen 2, zai kuma taimaka wajen dada inganta alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu.

Da yake karin haske ga taron manema labarai game da hakan, kakakin ma'aikatar Sun Jiwen, ya ambato wasu muhimman sassa na binciken wanda aka fara aiwatarwa a watan Nuwambar shekarar 2016, shi ne kuma irin sa na farko da kasar Sin ta yi hadin gwiwar aiwatarwa da wata kasa dake nahiyar Afirka.

Mr. Sun ya ce an bayyana kammalar wannan bincike ne, yayin ziyarar da mataimakin minista a ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Qian Keming ya kai tsibirin na Mauritius a ranar Laraba.

Sin ta yi amfani da damar wannan bincike na FTA, domin bude kofar ta ga kasashen duniya, ta yadda za a kara hade tattalin arzikin sassan duniya wuri guda, tare da karfafa hadin gwiwa da kasashe daban daban.

A yanzu haka dai Sin ta rattaba hannu tare da zartas da wasu yarjeniyoyi makamantan wadannan 14, tare da kasashe da yankuna har 22, dake sassan duniya daban daban.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China