in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jimillar cinikayya a tsakanin Sin da Afirka ta karu da kaso 22.2% a watanni biyar na farkon bana bisa na bara
2017-06-28 10:51:28 cri

Bisa alkaluman da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar, an ce daga watan Janairu zuwa watan Maya na bana, jimillar kudin shige da fice a tsakanin Sin da kasashen Afirka ta kai dala biliyan 70.14, adadin da ya karu da kashi 22.2 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara.

Cikin wannan adadi, kudin da aka samu daga safarar kaya zuwa Afirka ya kai dala biliyan 38.29, adadin da ya karu da kashi 7 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, yayin da adadin kudin da aka samu a fannin shigo da kaya daga nahiyar Afirka ya kai dala biliyan 31.85, wanda shi ma ya karu da kashi 47.8 cikin dari. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China