in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cinikayya ta yanar gizo a Sin za ta bunkasa da kaso 19 cikin 100 a 2017
2017-06-23 09:45:25 cri

Wani rahoto da kamfanin tuntuba na McKinsey ya fitar a jiya Alhamis, ya nuna cewa, harkar cinikayya ta yanar gizo a kasar Sin za ta bunkasa da kimanin kaso 19 cikin 100 a shekarar 2017 da muke ciki.

Rahoton ya kuma bayyana cewa, duk da kwan gaba kwan baya da fannin cinikayya ta yanar gizo yake fuskanta, kasar ta Sin ta shiga wani sabon karni a wannan fanni, lamarin da ya haifar da damammaki da bukatu masu tarin yawa, musamman ga wasu nau'in kayayyaki.

Rahoton ya ce, da dama daga masu sayar da kayayyaki ta yanar gizo wadanda ke kara shiga kafofin sada zumunta, sun gaza samar da hidima mai inganci, idan aka kwatanta da hidimar da wasu manyan shafukan cinikayya ta yanazr gizo ke samarwa

Alkaluma na nuna cewa, kasar Sin ce kan gaba a duniya a fannin cinikayya ta yanar gizo, daidai da girman manyan kasuwanni shida, ciki har da kasashen Amurka da Burtaniya da Japan, da Jamus da Koriya ta Arewa da kuma Faransa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China