in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 216 sun mutu a Kenya sakamakon cutar cholera
2016-04-09 13:57:27 cri
Ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya ta tabbatar da mutuwar mutane 216 daga watan Disambar bara zuwa yanzu a sakamakon barkewar cutar cholera.

Babban sakatare a ma'aikatar lafiyar kasar Nicholas Muraguri yace, kimanin 'yan kasar dubu 13 da 299 ne suka kamu da cutar a fadin kasar.

Sai dai yace gwamnatin kasar, ta dauki kwararan matakan dakile ci gaba da yaduwar cutar, tun bayan samun rahoton bullar cutar na farko a birnin Nairobi.

A cikin makon jiya, an samu sabbin bayanai na wadanda suka kamu da cutar kimanin 259, a wasu daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya na kasar.

Mahukuntan kasar sun bullo da wasu sabbin dabaru na binciko wadanda suka kamu da cutar a baya bayan nan, don daukar matakan dakile cutar cikin gagggawa, sannan an samar da kayayyakin tsabtace ruwan sha da kuma killace rijioji a matsayin wani bangaere na kandagarkin yaduwar cutar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China