in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwalara ta hallaka a kalla mutane 30 a kudancin Najeriya
2015-04-21 10:05:05 cri

Rahotanni daga jihar Delta dake kudu maso kudancin Najeriya, na cewa, cutar kwalara ta hallaka a kalla mutane 30, a yankin Isoko dake jihar ta Delta.

Da yake tabbatar da bullar wannan cuta a jihar, shugaban sashen lura da cututtuka masu bazuwa a asibitin gwamnatin jihar Dr. Steven Ofili, ya ce, matakan gaggawa da aka dauka domin dakile yaduwar cutar, sun taimaka matuka wajen kare bazuwarta.

Dr Ofili ya kara da cewa, cutar kwalara na bulla a yankin a kai a kai tun daga shekarar 2010, sakamakon gurbatar ruwan sha.

Bugu da kari likitan ya bayyana cewa, wasu daga al'ummun yankin kan gwammace amfani da magungunan gargajiya maimakon zuwa asibiti, wanda hakan kan jefa rayukansu cikin hadari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China