in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta dauki matakan dakile yaduwar cutar kwalara daga Sudan ta Kudu
2015-07-13 10:39:54 cri

Ma'aikatar lafiya ta kasar Sudan ta kara inganta matakan da take dauka na ganin cutar kwalara ba ta shigo cikin kasar ba daga yankunan kasar Sudan ta kudu.

Ministar lafiya ta kasar Somia Idris ta bayyana cikin wata sanarwa a jiya Lahadi cewa, yanzu haka kasar ta kafa wani dakin bincike na gaggawa a kan iyakar jihohin da ke makwabtaka da kasar don kai rahoton duk wani abu mai kama da ruwa-ruwa da ake zaton zawo ne. Ko da yake ya zuwa yanzu ba a samu rahoton bullar cutar a kan iyakar ko wace jiha ba.

Rahotannin baya-bayan nan na nuna cewa, kimamin mutane 484 ne suka kamu da cutar a kasar Sudan ta Kudu, ciki har da yara 'yan kasa da shekaru 5.

Ya zuwa yanzu mutane 29 ne dai cutar ta hallaka a Sudan ta Kudu da ke fama da yakin basasa tun karshen watan Disamban shekarar da ta gabata.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China