Kasar Sin ta tura sojojinta zuwa wani sansanin ba da tabbaci da kasar ta gina a kasar Djibouti, bisa kudurin da gwamnatocin kasar Sin da kasar Djibouti suka tsai da cikin hadin gwiwa. Wannan sansanin da aka gina a birnin Djibouti domin tabbatar da tsaron jiragen ruwa, kiyaye zaman lafiya da kuma ba da taimakon jin kai ga kasashen Afirka da yammacin Asiya, zai kuma ba da taimako wajen gudanar da atisayen sojoji, yin hadin gwiwar ayyukan soja da kuma ba da taimakon gaggawa a kasashen ketare da sauran ayyukan da abin ya shafa. (Maryam)