A lokaci guda, an yanke wa wasu mambobin kungiyar 'Yan Uwa Musulmi wato Muslim Brotherhood 3 hukuncin kisa, bisa aikata laifi makamancin na Mohamed Morsi.
Wannan shi ne karo na biyu da kotun kasar Masar ta yanke hukunci a kan Morsi.
Kafin jiyan, kotu ta taba yanke masa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan kurkuku, bisa laifin kamawa da dakatar da masu zanga-zanga ba tare da ka'ida ba, a watan Oktoban 2016.
Mohamed Morsi, wanda dan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ne, ya lashe babban zaben kasar Masar a shekarar 2012, sa'an nan ya zama zababben shugaba na farko a tarihin kasar.
Sai dai shekara daya bayan hawa karagar mulki, sai aka fara samun zanga-zangar adawa da gwamnatinsa, lamarin da ya sanya sojojin kasar hambarar da shi.
Daga bisani kuma aka sanya kungiyar ta'Yan Uwan Musulmi cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
Haka zalika an zargi mista Morsi da aikata laifukan fasa gidan yari, da leken asiri, da dai sauransu.(Bello Wang)