in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta yi watsi da rahotannin dake cewa tsohon shugaban Zimbabwe na neman mafaka a kasar
2017-11-24 09:04:08 cri
Gwamnatin Zambia ta yi watsi da rahotannin dake cewa tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe na neman mafaka a kasar.

Rahotanni dake yawo a shafukan sada zumunta na zamani na cewa tsohon shugaban mai shekaru 93 na duba yiwuwar neman mafaka a Zambia, bayan mulkin da ya shafe shekaru 37 yana yi ya kawo karshe.

Sai dai Ministan harkokin wajen Zambia Harry Kalaba, ya ce Mugabe bai tunkari Gwamnatin Zambia da batun ba, ya na mai cewa rahotannin zargi ne kawai.

Ya ce babu wani da ya tuntubi Gwamnatin kasar da batun, cikin Mugabe ko wakilansa.

Wasu rahotannin na cewa tsohon Shugaban ba shi da muradin barin kasar.

Ana dai sa ran shugaban na Zambia Edgar Lungu, zai isa Zimbabwe a yau Juma'a domin halartar bikin kaddamar da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa.

Ministan Harkokin wajen Zambia ya ce Edgar Lungu ya yanke shawarar halartar bikin ne domin kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China