Mr Felix wanda ya tabbatar da hakan a jiya Alhamis, ya ce gwamnatin Zambia na da tabbacin cewa, cikin 'yan makonni masu zuwa, asusun na IMF zai fito da rahoton tattaunawar da mahukuntan kasar suka yi don mikawa hukumar darektocin asusun.
Ya ce, tattaunawar da sassan biyu suka yi, ta kuma yi la'akari da irin ci gaban da aka samu karkashin shirin gwamnati na farfado da tattalin arzikin kasar da kuma shirin raya kasa daga shekarar 2017 zuwa 2019.(Ibrahim)