in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zambia ta kaddamar da aikin babban titin da kasar Sin ta bada kudin aiwatarwa
2017-09-09 13:39:15 cri

Kasar Zambia ta kaddamar da aikin babban titin da kasar Sin ta bada kudin ginawa, wanda zai hada sassan kudu da arewacin kasar zuwa garuruwan hakar ma'adanai dake lardin Copperbelt.

Kamfanin fasaha na Jiangxi na kasar Sin wato CJIC a takaice, shi ne zai yi aikin ginin tagawayen titin Lusaka zuwa Ndola, mai tsawon kilomita 321, a kan kudi dala biliyan 1.2 da bankin Exim na kasar Sin ya bada rancensu.

Aikin titin da aka kaddamar a jiya Jumma'a, wanda zai dauki tsawon shekaru 4, zai samar da guraben aikin yi ga mazauna yankin sama da 3,000.

Da yake jawabi lokacin kaddamar da aikin a lardin Chisamba dake tsakiyar kasar, Shugaban Zambia Edgar Lugu, ya ce ginin titin zai inganta zirga-zirgar ababen hawa tare da rage hadduran da ake yawan samu a dan karamin titin.

Ya kuma bayyana irin dimbin alfanu da za a samu ta fuskar tattalin arziki, inda ya ce yana da matukar muhimmanci ga ababen hawa dake ratsawa ta kasar, wadanda ke zirga–zirga a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da sauran kasashen dake yankin kudancin Afrika.

A nasa bangaren, Jakadan kasar Sin a Zambia Yang Youming, cewa ya yi, ginin tagwayen titin zai mayar da kasar cibiyar sufuri a yankin.

Ya kara da cewa, kasashen biyu sun hada hannu sosai wajen samar da kayakin more rayuwa cikin shekaru da dama, yana mai cewa kasar Sin za ta ci gaba da mara baya ga yunkurin raya Zambia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China