in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya taron musaya kan samar da guraban aikin yi ga daliban kasashen Afirka dake karatu a nan kasar Sin
2017-11-23 13:11:44 cri

Kwanan baya ne a nan birnin Beijing, aka shirya wani taron musaya na musamman game da samar da guraban aikin yi ga daliban kasashen Afirka dake karatu a nan kasar Sin, masana a wannan fannin sun nuna cewa, shawarar 'Ziri daya da hanya daya' ta taimakawa kamfanoni da dama a kasar Sin zuwa kasashen Afrirka, a sa'i guda kuma 'yan kasashen Afirka dake neman karatu a kasar Sin suna ta karuwa, bisa wannan yanayin da ake ciki, wannan taron musaya na da ma'ana kwarai wajen inganta matakan kamfanonin kasar Sin na habaka ayyukansu a Afirka, kana da taimakawa matasan Afirka wajen samun ayyukan yi.

An shirya wannan taron musaya ne a karkashin hadaddiyar kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama'ar kasar Sin, da jami'ar koyon ilmin tattalin arziki da cinikayya da kasashen ketare ta kasar Sin. A yayin da suke ambaton damar samun aikin yi da kamfanonin kasar Sin za su iya samarwa a nan gaba, daliban kasashen Afirka dake karatu a nan kasar Sin suna sa ido sosai a kai.

'Ina fatan na samu aikin yi a fannin cinikayyar kasa da kasa'.

'Aikin da nake fatan yi shi ne a fannin nazari da bunkasa kaya.'

Dalibai da yawa sun yi farin ciki yayin da suke ziyartar rumfunan kamfanonin kasar Sin daban daban, don bayyana yanayin da suke ciki da Sinanci sosai.

Rahotanni na cewa, akwai daliban kasashen Afirka kusan 400 dake karatu a kasar Sin da suka halarci wannan taron musayar. Kafin haka, akwai dalibai kimanin 1000 da suka fito daga kasashen Afirka 52 da suka riga suka wallafa takardun bayyanansu ta yanar gizo. Wadannan daliban za su yi takarar neman samun aikin yi a kamfanoni 66 na gwamnati, da kananan hukumomi, da masu zaman kansu na kasar Sin suka samar, cikin guraban ayyukan yi kusan 500 da aka tanadarwa kasashen Afirka.

Wani injiniya a kamfanin gine-gine da harkokin sadarwa na kasar Sin, wato CCCC a takaice, mista Fu Jiawei ya ce, kamfaninsa na neman daliban kasashen Afirka dake da ilmi a fannin aikin gine-gine, a ganin sa, daliban Afirka dake karatu a nan kasar Sin suna da fifiko a wannan fannin.

'Saboda sun fito ne daga kasashen Afirka, don haka suna iya ba da taimako sosai yayin da kamfaninmu ke gudanar da ayyuka a kasashensu. Na yi imanin cewa, sun fi Sinawa wajen hada kai da al'ummar wurin, wannan ya sa suke samun saukin gudanar da ayyukansu a wurin, tare kuma da dacewa da yanayin wurin.'

Wata masaniyar tattalin arziki a kamfanin gina layin dogo na kasar Sin wato CRGL a takaice, madam Ye Shuang tana ganin cewa, idan kamfanonin kasar Sin suna fatan habaka kasuwanni a kasashen ketare, ciki har da kasashen Afirka, dole ne su yi amfani da ma'aikatan wurin, don haka daliban kasashen dake karatu a kasar Sin su ne suka fi dacewa a wannan fannin.

'Na farko shi ne suna iya Sinanci, sa'annan sun san harsunan kasashensu sosai, abin da ya fi muhimmanci shi ne, suna da ilmi a fannoni daban daban, wannan shi ne abun da muke bukata kwarai. Wadannan dalibai, ban da harsuna ma suna da ilmi a fannonin aikin gine-gine, kula da masana'antu da kasuwanni, kwamfuta, dokokin kasa da kasa, cinikayyar kasa da kasa da dai sauransu, dukkansu kwararru ne da muke bukata wajen habaka kasuwar kasa da kasa.'

Bisa kididdigar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar, na nuna cewa, ya zuwa yanzu, kamfannonin kasar Sin dake kasashen Afirka sun wuce 3100, daliban kasashen Afirka dake karatu a kasar Sin, ciki har da wadanda suka samu kudaden alawus, da wadanda suka biya kudin karatunsu da kansu sun wuce dubu 60.

Mataimakiyar shugabar hadaddiyar kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama'ar kasar Sin, madam Lin Yi ta bayyana cewa, an shirya wannan taron musaya kan samun aikin yi ne da nufin taimakawa kamfanonin kasar Sin wajen samun kwararrun wurin da suka dace, kana da taimakawa matasan kasashen Afirka wajen samun aikin yi.

'Kungiyarmu ta kafa wata gada a tsakaninsu, ta yadda wadannan dalibai dubu 60 suna iya samun damar neman aikin yi, yayin da kamfanonin kasar Sin fiye da 3000 suna iya samun damar daukar ma'aikatan wurin aiki.'

Wani rahoto da MDD ta fitar ya nuna cewa, jimilar al'ummar nahiyar Afirka za ta kai kimanin biliyan 1.2, nan da shekarar 2025, kuma yawan matasan nahiyar zai kai kashi 1 cikin hudu bisa na matasan duk duniya baki daya.

Babbar manazarciyar sashen nazarin harkokin Afirka na kwalejin nazarin kimiyyar zaman takewar al'ummar kasar Sin, madam He Wenping ta ce, samar da guraban aikin yi muhimmiyar hanya ce ta warware matsalar rashin samun aikin yi da matasan nahiyar ke fuskanta amma ba dogaro da samun ilmi kawai ba.

Bayanai na nuna cewa, a yayin taron musayar, hadaddiyar kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta jama'ar kasar Sin da jami'ar koyon ilmin tattalin arziki da cinikayya da kasashen ketare ta kasar Sin sun sa hannu kan wata yarjejeniyar hadin kai bisa manyan tsare-tsare, da nufin inganta musayar ra'ayoyin ba da ilmi da ci gaban matasa a tsakanin Sin da kasashen ketare. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China