Jiya Litinin ne, aka bude wani gaggarumin bikin fina-finan kasa da kasa na Sin da Afirka karo na farko a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu, za a shafe kwanaki 3 ne ana yin bikin. Bikin ya hallara mutane kusan 500, ciki har da fitattun masu aiki a fannin da suka fito daga kasashen Sin, Afirka ta kudu, Najeriya, Tanzania, Ghana, Namibia da kuma Botswana da dai sauransu, kana da wasu baki daga bangarori daban daban, inda suka ba da shawarwari kan yadda za a hada kai tare da ciyar da harkar fina-finan na Sin da kasashen Afirka gaba. Baya ga haka, yayin bikin za a nuna wasu muhimman fina-finan bangarorin biyu, wadanda ke nuna nasarorin da aka samu a sana'ar fina-finan Sin da Afirka, da cin gajiyar fasahohin da suka samu a fannin.
A sakonsa na fatan alheri ga bikin, shugaban kwamitin shirya bikin, kuma shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI mista Wang Gengnian ya ce, a kokarin da masu sana'ar fina-finan bangarorin biyu suke yi, bikin zai kasance wani dandali mai kyau wajen nuna yadda ake tsara fina-finai, da yadda ake darajanta al'adun al'umma musamman na bangarorin biyu. (Bilkisu)