Ezra Sakawa, babban daraktan lafiya na babban asibitin Mubi, ya shedawa manema labarai cewa, asibitin ya karbi wadanda harin ya rutsa da su kimanin 48, kuma 8 daga cikinsu sun mutu a lokacin da ake kokarin duba lafiyarsu.
Wani jami'in dan sandan yankin ya ce mutune 50 ne suka mutu a ranar Talata, ya kara da cewa, wani matashi ne wanda ba'a gano shi ba ya kaddamar da harin kunar bakin waken a cikin masallacin garin Mubin jahar Adamawa da yammacin ranar Talata.
Maharin ya tayar da bama boman ne bayan idar da salla a cikin masallacin.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayi Allah wadai da harin kunar bakin waken, inda ya bayyana harin a matsayin abin takaici kuma abin Allah wadai.(Ahmad Fagam)