in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka ya sanar da kama wani mutumin da aka zargi da kai hari kan karamin ofishin jakadancin kasar dake Banghazi
2017-10-31 13:34:09 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a jiya ranar 30 ga wata cewa, sojojin kasar Amurka sun kama wani mutum da aka zargi da kai hari ga karamin ofishin jakadancin Amurka dake Banghazin kasar Libya a ranar 29 ga wata.

Trump ya bayyana a cikin sanarwa cewa, kasar Amurka ba za ta dakatar da neman masu shiryawa, da kai hari a Banghazi ba, za kuma ta gurfanar da su a gaban kotu.

Trump kara da cewa, kasar Amurka za ta ci gaba da nuna goyon baya ga gwamnatin kasar Libya a kokarin ta na yaki da ta'addanci, da tabbatar da kasar ba ta kasance mafakar 'yan kungiyar ta'addanci irin IS ba.

A ranar 11 ga watan Satumba na shekarar 2012 ne aka kai hari kan karamin ofishin jakadancin kasar Amurka dake Banghazi, wanda ya haddasa mutuwar Amurkawa 4 ciki, har da jakadan kasar Amurka dake kasar ta Libya Christopher Stevens. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China