Dukkanin kasashe membobin MDD 193 ne sun jefa kuri'un yayin babban taron MDD karo na 72, inda aka samu kuri'un amincewa guda 191, yayin da Amurka da Isra'ila suka jefa kuri'ar na ki. Wannan shi ne karo na 26 da aka zartas da irin wannan kudiri a wajen babban taron MDD.
Kudirin ya sake kira ga dukkanin kasashe, da kada su amince da wata doka ko matakan sanyawa kasar Cuba takunkumi, tare kuma da sake bukatar kasashen da har yanzu suke daukar irin wannan matakai da su soke tare da kawo karshensu.
Kasar Amurka ta dade tana jefa kuri'ar na ki game da kudirin soke takunkumin da aka sanyawa Cuba. A bara, yayin da ake samun kyautatuwar alaka tsakanin Amurka da Cuba, Amurka ta jefa kuri'ar janye jiki. Amma bayan Donald Trump ya dare kan karagar mulki, sai aka sake ci gaba da zaman doya da manja tsakanin kasashen biyu.(Murtala Zhang)