in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya halarci taron koli na kwamitin sulhun MDD mai kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya
2017-09-21 11:14:51 cri
A jiya 20 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron koli na kwamitin sulhun MDD mai kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya a birnin New York dake kasar Amurka.

Wang Yi, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, Sin ta nuna goyon baya ga yin kwaskwarima kan ayyukan kiyaye zaman lafiya don gudanar da ayyukan yadda ya kamata. Kamata ya yi a yi kwaskwarima bisa ka'idojin ikon mallakar kasa, da gujewa tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasashe, da warware rikice-rikice cikin lumana.

Wang Yi ya bayyana cewa, wasu kasashen Afirka suna fuskantar kalubale yayin da suke kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaronsu. Ya kamata kasa da kasa musamman MDD su zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kungiyar AU a fannin kiyaye zaman lafiya, da samar da gudummawa ga kungiyar AU cikin lokaci. Na farko, ya kamata a kara nuna goyon baya ga kasashen Afirka a fannin siyasa, wato warware matsalolinsu ta hanyar lumana, da zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da kungiyar AU wajen magance rikici, da tinkarar rikici da kuma sake ginawa bayan barkewar rikici. Na biyu, ya kamata a kara nuna goyon baya ga kungiyar AU wajen inganta karfinsu a dukkan fannoni bisa bukatun kungiyar. Na uku, ya kamata a kara samar da kudi gare su, Sin ta nuna goyon baya ga shirin samar da kudi ga ayyukan kiyaye zaman lafiya da kungiyar AU ta gabatar. Ta kuma yi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya gabatar da shirin nuna goyon baya ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na kungiyar AU bisa kuduri mai lamba 2320 da mai lamba 2378 cikin hanzari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China