Wang Yi ya bayyana cewa, Sin da kasashen Afirka sun kasance abokai masu buri iri daya da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Kamata ya yi kasar Sin da kasashen Afirka su kara hadin gwiwa da juna, da yin amfani da fifikonsu wajen raya kansu da hadin gwiwar Sin da Afirka, da canja damar hadin gwiwa zuwa sakamakon hadin gwiwa. Ya kamata a aiwatar da sakamakon taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da sa kaimi ga shirye-shiryen hadin gwiwa guda 10, da kara azama kan aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", ta haka kasashen Afirka za su ci gajiya sosai.
A cikin jawabinsu, ministocin harkokin wajen kasashen Afirka sun nuna godiya ga kasar Sin domin ta samar da gudummawa ga kasashen Afirka a dogon lokaci, da nuna goyon baya ga shawarar "ziri daya da hanya daya", da nuna yabo ga kasar Sin domin ta aiwatar da sakamakon taron koli na Johannesburg na dandalin tattaunawar, kuma suna fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, da samun moriyar juna da bunkasuwa mai dorewa. (Zainab)