A wata sanar da hukumar sojin kasar ta fitar a jiya Asabar ta ce, wadannan rundunoni 19 za'a kasata zuwa bangarori 6 ne, wadanda suka hada da dakarun tsaron kasa, da injiniyoyi, da masu gadi, da masu kai daukin gaggawa, da kuma matuka jirage masu saukar ungulu.
Kasar Sin ta yi rajistar rundunar kiyaye zaman lafiya mai karfin dakaru dubu 8, wadanda ke aiki da MDD a watan Satumba, kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar ta tabbatar da hakan.
A halin yanzu, rundunar sojin Sin tana da bataliyoyi kimanin 9 wadanda ke aiki karkashin shirin kiyaye zaman lafiya na MDD, wanda ya kai kaso 91.5 na dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Sin.
Da kafa wadannan kananan rundunonin ko-ta-kwana, dakarun kiyaye zaman lafiya na kasar Sin za ta kara karfi a kokarin da take na kai daukin gaggawa yadda ya kamata, kamar yadda You Haitao, mataimakin kwamanda rundunar PLA ya tabbatar da hakan.
A kalla ma'aikatan kasar Sin maza da mata dubu 36 ne suka yi aiki karkashin shirin kiyaye zaman lafiya na MDD, yayin da 13 daga cikinsu suka sadaukar da rayuwarsu cikin shekaru 27 da suka gabata. (Ahmad Fagam)