Xie, ya bayyana cewa, daftarin bayanan da aka cimma matsaya kansu sun tabo dukkan muhimman batutuwa dake kunshe cikin yarjejeniyar da aka kulla a birnin Paris game da sauyin yanayi.
Taron na COP 23 ya fayyace tsarin da ya kamata a bi wajen shirya taron tattaunawar shekarar 2018, kana ya amince da a hanzarta aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayin gabanin shekarar 2020, da kuma daukar matakan takaita fitar da hayaki mai gurbata yanayi.
Wakilin na Sin ya ce, sauye sauye da kuma fitar da managartan tsare tsaren da kasashen da suka halarci taron suka yi ya aza wani harsashe wanda zai tabbatar da cimma nasarar aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris kamar yadda aka tsara tun da farko. Ya kara da cewa suna fata dukkan bangarorin da abin ya shafa za su mutunta tsarin daidaito, kuma za su amince da sauke nauyin dake wuyansu, kana su bi dukkan sharrudan dake wuyan kowace kasa don tabbatar da ganin an cimma nasarar aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris yadda ya kamata. (Ahmad Fagam)