Xie Ji, mataimakin babban wakilin kasar Sin a taron karawa juna sani na COP22 da ake gudanarwa a birnin Marrakech na kasar Morocco, ya bayyana cewar, akwai bukatar dukkanin bangarorin da abin ya shafa su cimma matsaya game da aiwatar da yarjejeniyar Paris.
A taron MDD kan sauyin yanayi a karon farko da aka gudanar tun bayan amincewa da yarjejeniyar Paris, wanda aka gudanar kwanaki 3 da suka gabata, an bude taron na COP22 ne da safiyar ranar Litinin, mahalarta kusan dubu 20 ne daga sassan duniya da dama, wadanda ake sa ran za su tattauna na tsawon kwanaki 11, game da batutuwan da suka shafi yadda za'a aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris cikin nasara. (Ahmad Fagam)