in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
COP ya ba da gudummawa sosai wajen kara ilimantar da al'umma kan tinkarar sauyin yanayin duniya
2016-11-09 11:26:08 cri

Tsohon ministan muhalli na kasar Peru kana jami'in kula da manufofin tinkarar sauyin yanayin duniya da makamashi a asusun kare albarkatun kasa Mr. Manuel Pulgar Vidal ya bayyana a yayin wani taron karawa juna sani game da tinkarar sauyin yanayin duniya da aka shirya jiya Talata a birnin Marrakech na kasar Morocco cewa, babban taron tinkarar sauyin yanayin duniya na MDD, COP ya taimaka sosai wajen kara ilimantar da al'umma game da kokarin da ake yi na tinkarar sauyin yanayin duniya.

Mr. Manuel Vidal yana ganin cewa, ko da yake ba a samu sakamako mai kyau kamar yadda ake fata a yayin babban taron tinkarar sauyin yanayin duniya ba, a saboda haka, za a gamu da wasu matsaloli iri iri a lokacin da ake tattaunawa da kuma aiwatar da manufofi da matakan da za a dauka, amma duk da haka ba za a yi watsi da muhimmiyar ma'anar wannan babban taron ba. Mr. Manuel Vidal ya ce, "Dukkan manyan tarukan tinkarar sauyin yanayin duniya na MDD da aka yi, ko za a yi, ko shakka babu, sun zama ko za su ci gaba da zama wani dandalin yin shawarwari kan yadda za a tinkari sauyin yanayin duniya kai tsaye a tsakanin gwamnatoci daban daban. Bugu da kari, wasu mahalarta taron wadanda ba sa wakiltar kowace kasa sun dauki tarin matakan tinkarar sauyin yanayin duniya, a ganina, za su taka muhimmiyar rawa a yayin babban taron tinkarar sauyin yanayin duniya na MDD. Bayan irin wannan babban taron da aka yi a birnin Copenhagen, an gane cewa, yarjejeniyoyi da takardu kawai, ba za su gamsar ba. Hakkin mu ne mu kara ilimantar da al'ummomin duniya muhimmancin tinkarar sauyin yanayin duniya."

Idan ana ganin cewa, shawarwarin da ake yi a yayin babban taron tinkarar sauyin yanayin duniya tamkar takkadamar siyasa ce kawai, to, wannan kuskure ne. Yanzu, ana gane cewa, sauyin yanayin duniya yana tasiri a bayyane ga zaman rayuwar al'umma. Sakamakon da aka samu ko za a samu a yayin manyan tarukan tinkarar sauyin yanayin duniya za su yi tasiri matuka ga 'yancin kowane mutum a duniyarmu ga 'yancinsu na neman samu ci gaba. Sakamakon haka, wadanda suke da ikon tsai da kuduri suna bukatar bincike tare da nazarin abubuwa iri daban daban kafin su tsai da duk wani kuduri.

Madam Frances Way, jami'a ta farko a shirin kawar da sanadarin Carbon ta fadi albarkacin bakinta a yayin taron, inda ta ce, "A ganina, kokari tinkarar sauyin yanayin duniya, ba batu ne na siyasa kawai ba, al'amari ne na tattalin arziki, sabo da sauyin yanayin duniya yana kawo illa ga masu zuba jari da harkokin kasuwanci. Sauyin yanayin duniya yana da alaka da kowane mutum, akwai bukatar kowa ya ba da nasa kokarin. Mai yiyuwa ne wasu sana'o'i da masana'antu za su fuskanci matsala a lokacin da ake rage yin amfani da sinadarin Carbon, amma ina tsammani wannan wani mataki ne da bai kamata a yi watsi da shi ba."

Ko shakka babu, akwai bukatar kowa ya ba da gudummawa a kokarin da ake yi na tinkarar sauyin yanayin duniya. Mr. Ramiro Fernandez, direkta mai kula da manufofin tinkarar yanayin duniya na asusun Avina, wato kungiyar dake kula da muhallin ruwa na yankin Latin Amurka, ya bayyana cewa, "Ya kamata mu tabbatar da ganin an dauki matakan tinkarar sauyin yanayin duniya a shiyoyyin yankunan al'umma marasa arziki. Ya zuwa yanzu, al'ummomin dake yankuna masu arziki ne suke kokarin daukar matakan tinkarar sauyin yanayin duniya. Amma akwai bukatar kara mai da hankali wajen kara karfin manoma wajen tinkarar sauyin yanayin duniya." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China