Taron na da nauyin samar da hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar wadda kusan dukkan kasashen duniya suka amince da ita a shekarar 2015.
Yarjejeniyar ta Paris na da nufin magance matsalolin sauyin yanayi ta hanyar rage fitar da gurbatacciyar iska tare da sanya matsakaicin mataki na ganin yanayin zafin duniya bai dara yanayin da yake kafin zuwa masana'antu da maki biyu na ma'aunin Celsius ba.
Yayin bude taron, Sakatariyar zartarwa ta hukumar kula da sauyin yanayi ta MDD Patricia Espinosa ta ce, "idan aka hada yarjejeniyar da muradun ci gaba masu dorewa, to akwai tartibiyar hanya ta magance sauyin yanayi da samar da dawwamammen ci gaba."
Da take zayyana ayyukan da gwamnatocin kasashe za su shawo kansu yayin taron na Bonn, ta ce manufar ita ce, daukar managartan matakan tabbatar da kammala tsare-tsare ayyukan yarjejeniyar a kan lokaci, tare kuma da karfafa hanyoyin aiwatar da ita.
Yayin wani taron manema labarai gabanin bude taron, wakilin musammam na kasar Sin kan batun sauyin yanayi Xie Zhenhua ya ce kasarsa na fatan maharlarta taron za su samar da hanyoyin dake bayyana abubuwan da ake bukata daga dukkan bangarorin dake cikin yarjejeniyar ta Paris. (Fa'iza Mustapha)