Magadan garin birane fiye da 60 na kasar Amurka sun gabatar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suke ki amincewa da kudurin da shugaban kasar Turmp ya dauka, ciki har da magadan garin manyan biranen kasar kamar Los Angeles, New York, Salt Lake, Pittsburgh da sauransu. Magadan garin sun bayyana cewa, jama'a fiye da miliyan 36 dake biranensu za su amince da girmama yarjejeniyar Paris, tare da cika alkawarin da aka dauka a cikin yarjejeniyar. (Zainab)