in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da janye daga yarjejeniyar Paris
2017-06-02 13:48:19 cri
A jiya ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar a fadar White House cewa, kasar Amurka za ta janye daga yarjejeniyar Paris ta tinkarar matsalar sauyin yanayi na duniya.

Shugaba Trump ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, yarjejeniyar Paris ta rage moriyar kasar Amurka da kara baiwa sauran kasashe moriya.

Wasu bangarorin kasar Amurka da kasashen waje sun yi suka kan matsayin gwamnatin Trump a kan batun yanayi.

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, kasar Amurka ta shiga kungiyar kasashen da ba sa son kyakkyawar makoma ga duniyarmu.

Magajin garin birnin Pittsburgh na kasar Amurka ya bayyana a kan shafinsa na twitter cewa, jama'ar birnin za su ci gaba da martaba yarjejeniyar Paris don tinkarar sauyin yanayi.

A wannan rana, babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayar da sanarwa ta hannun kakakinsa cewa, abin bakin ciki ne da kasar Amurka ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar Paris game da kokarin rage fitar da iskar da ke dumama yanayi da tabbatar da tsaron duniya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a jiya ranar 1 ga wata cewa, koda ya ke wasu kasashe sun canja matsayinsu, amma Sin za ta ci gaba da daukar matakai don tinkarar sauyin yanayi tare da martaba yarjejeniyar Paris. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China