Kafin yin garam-bawul din, Mnangagwa shi ne ke rike da mataimakin Mugabe a shugabancin jam'iyyar ZANU-PF mai mulkin kasar, kuma shi ne mataimakin shugaban kasar, kana ministan shari'a na kasar.
Tsohon ministan harkokin cikin gidan kasar Ignatius Chombo shi ne aka baiwa mukamin ministan kudin kasar, yayin da babban jami'in hukumar leken asirin kasar Happyton Bonyongwe shi ne aka nada a matsayin sabon ministan shari'a na kasar.
Tsohon ministan tsara tattalin arzikin kasar Obert Mpofu shi ne sabon ministan harkokin cikin gidan kasar, yayin da Patrick Zhuwao, baffa ne ga Mugabe wanda a baya yake rike da mukamin ministan matasa na kasar yanzu ya koma sabon ministan kula da ayyukan gwamnati da walwalar al'umma.
Garam bawul ga majalisar ministocin Zimbabwe ya zo ne a yayin da ake jajiberin zaben shugaban kasar, wanda za'a gudanar a shekarar 2018, inda shugaba Mugaben zai sake tsayawa takara a zaben. A shekarar 2015 ne Mugabe ya gudanar da gyaran fuska ga majalisar ministocinsa na karshe. (Ahmad Fagam)