in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
LeBron James ya jinjinawa sabon tauraron kungiyar Lakers
2017-11-15 17:41:13 cri
Zakaran kwallon Kwando a gasar NBA LeBron James, ya jinjinawa sabon tauraron kungiyar Lakers Lonzo Ball, wanda ya kafa sabon tarihin zura kwallaye a ragar abokan hamayya, a wasan kungiyar da Milwaukee Bucks na ranar Asabar din karshen makon jiya.

A ranar Litinin ne dai LeBron James, ya gabatar da sakon na sa na taya murna ga Ball, wanda a shekarun haihuwar sa 20 da kwanaki 15, ya zamo dan wasan kungiyar Lakers mafi yarinta, da ya karya matsayin bajimtar 'yan wasan ta, inda ya ci wa kungiyar maki 19, ya taimaka wajen samun wasu makin 13, ya karbe kwallo 12, ya tare 4 da kuma dakatar da 3 a wasa daya.

Wannan nasara ta Ball dai ta zarce wadda shi kan sa LeBron James ya kafa, a kakar wasa ta 2004 zuwa 2005. Kungiyar Lakers ta tabbatar da cewa, rabon da wani dan wasan ta ya cimma irin wannan nasara, tun lokacin tauraron ta Michael Jordan, wanda ya kafa tarihin hakan a shekarar 1985.

Gabanin wasan ranar Litinin da Lakars din ta buga da New York Knicks, James ya shaidawa kafar talabijin ta ESPN cewa, kwarewar Ball ta tuna masa irin hazakar da shi kan sa ya nuna sama da shekaru 10 da suka gabata, lokacin da ya kasance dan wasa daya tilo da ya zarce daga makarantar sakandare zuwa gasar da hukumar NBA ke shiryawa, wanda daga nan ne kuma ya samu daukaka mai tarin yawa a fagen kwallon kwando.

LeBron James ya ce " ina ganin zai kasance dan wasa mai hazaka, zai bada gudummawa mai tarin yawa ga kungiyar mu, mai yiwuwa ma ya zarce sa'a a wannan fage, idan har ya ci gaba da irin wannan himma, wanda ga dukkanin alamu zai iya cimma nasarar hakan."(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China