in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kwallon Kwando ajin mata ta Najeriya D'Tigress ta samu nasarar lashe gasar nahiyar Afirka ajin mata ta bana
2017-09-21 09:29:21 cri

Kungiyar kwallon Kwando ajin mata ta Najeriya D'Tigress, ta shiga jerin manyan kungiyoyin kwallon Kwando na duniya, karkashin inuwar hukumar dake lura da wasan ta kasa da kasa FIBA.

Kungiyar ta D'Tigress ta daga da matsayi 8, inda a yanzu ta kai ga matsayi na 34 a duniya, bayan da ta samu nasarar lashe gasar nahiyar Afirka ajin mata ta bana, gasar da ta gudana a birnin Bamako na kasar Mali. A bara D'Tigress din na matsayi na 42 ne a duniya.

'Yan wasan na Najeriya dai sun lashe dukkanin wasannin da suka buga guda 8, wanda hakan ya ba su damar daga kofin na bana. Yanzu haka D'Tigress ce ta 5 a nahiyar Afirka, inda take biye da Senegal mai matsayi na 17 a duniya, da Angola dake da matsayi na 18, da Mali mai matsayi na 24, yayin da kuma kasar Mozambique ke da matsayi na 25 a duniya.

A gasar nahiyar ta bana, D'Tigress din ta doke Senegal har karo biyu, ta kuma lallasa Mali a wasan kusa da kusan na karshe.

Da yake tsokaci game da ci gaban da kungiyar ta samu a bana, shugaban hukumar dake kula da kwallon Kwando ta Najeriya NBBF injiniya Musa Kida, ya ce hakan sakamako ne na irin sauye sauye da suke gudanarwa a sha'anin wasan kwallon kwando.

Ya ce sai da suka ci kwakwa kafin su kai ga doke Mali. Kuma daukar kofin gasar bayan shekaru 12 suna hankoro, ba abu ne mai sauki ba. Injiniya Kida ya kara da cewa, fatan sa shi ne ganin kungiyar ta kai matsayi na koli a duniya baki daya.

Kasashen dake kan gama yanzu haka a duniya baki daya dai, su ne Amurka, da Sifaniya, da Faransa, da Australia, da Canada, da Czech Republic, da Turkiyya, da Serbia, da Brazil da kuma kasar Sin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China