Mugabe ya bayyana hakan ne a babban taron MDD inda ya bayyana halin da ake ciki game da cigaban kasashen duniya da cewa ya sha banban ta fuskoki da dama musamman idan aka yi la'akari da yadda wasu ke kallon cigaban duniya a matsayin buri, juyin-juya-hali, sauya fasali, gama-gari, wanda ya shafi dukkannin fannonin rayuwar bil adama.
Wannan ne dalilin da yasa ajandar ke bukatar hada karfi da karfe da dunkulewa waje guda, da yin aikin tare da kuma hadin kai, inji mista Mugabe.(Ahmad Fagam)