Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin, shugaba Akufo-Addo ya ce, shirin zai baiwa yara da dama damar zuwa makarantar sakandare, bayan da gwamnati ta soke biyan wasu kudaden makaranta.
Ya ce, gwamnati ta kaddamar da wannan shiri ne da zummar rage yawan yaran da ba su da sukunin zuwa makaranta a fadin kasar ta Ghana. Kuma matakin ba zai mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na gina kasar ba.
Kimanin dalilai 400,000 ne dai ake saran za su ci gajiyar shirin, wanda aka fara aiwatarwa tun a ranar Litinin.
Yanzu dai gwamnati ta daukewa daliban biyan kudin makaranta da sauran kudade da suka shafi harkar karatu da dalibai ne ke biya a can baya.(Ibrahim)