in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da bikin kwalejin Confucius a kasar Ghana
2017-10-01 13:46:21 cri
A ranar Asabar ne kwalejin Confucius dake jami'ar kasar Ghana ta gudanar da wani kasaitaccen bikin ranar kwalejin Confucius ta duniya, wanda aka gudanar a Accra babban birnin kasar.

Dalibai da dama sun gudanar da wasannin da suka burge 'yan kallo da suka hada da rera wakoki nau'i daban daban, da raye-raye, da yin darussan harshen Sinanci, yayin da wasu daga cikin masu ziyarar bikin suka dandana shayin Sinawa, da ganewa idonsu wasu al'adun gargajiyar kasar Sin da suka hada da yin fenti a fuskoki iri na wasan kwaikwayon gargajiya na Peking.

Jakadar kasar Sin a Ghana Sun Baohong, ta yi amanna cewa, muddin al'ummomin kasashen biyu suka hada hannu don yin aiki tare da juna, za'a samu matukar bunkasuwar ilmi da cudanyar al'adu a tsakanin bangarorin biyu, kuma hakan zai yi tasiri ga al'ummomin kasashen biyu masu zuwa a nan gaba.

Ta bukaci daliban dasu yi aiki tukuru, kana su tallafawa dukkan hanyoyin da zasu karfafa kyakkyawar abokantaka tsakanin kasashen biyu.

Daraktar kwalejin Mei Meilian, ta bayyana cewa, zata yi aiki tukuru wajen sauke nauyin dake wuyanta ta hanyar shirya darrusan koyan harshen Sinanci, da koyar da al'adun Sinawa ga 'yan kasar ta Ghana, kana tace zata taimaka wajen ganin an baiwa yan kasar ta Ghana karin guraben karo ilmi a kasar Sin da kuma bayar da damammakin yin ziyara a kasar ta Sin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China