in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kudu ta musanta taimakawa 'yan tawayen Sudan
2017-11-03 09:46:39 cri
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit, ya karyata zargin da ake yiwa kasarsa na tallafawa kungiyoyin 'yan tawayen kasar Sudan masu dauke da makamai.

Kiir yace, wannan jita-jita ce marar tushe, ya kara da cewa babu wani dalili da zai sanya kasarsa ta taimakawa kungiyoyin 'yan tawayen kasar Sudan, kasancewar Sudan ta kudu ba cibiya ce dake samar da makamai ba.

Yace idan ma har ana son a yi zargi ne, ana kuma iya zargin kasar Sudan wajen taimakawa 'yan tawayen Sudan ta kudun wajen samar musu da makamai, Kiir ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Sudan, Omar al-Bashir.

A nasa bangaren, Al-Bashir, ya nanata cewa kasarsa ba zata taba goyon bayan wata kungiyar 'yan tawaye masu dauke da makamai a Sudan ta kudu ba, yace taimakawa 'yan tawaye babu abin da zai haifar sai tada hargitsi, da rashin zaman lafiya da rikice-rikice a kan iyakokin kasashen biyu.

Al-Bashir ya jaddada aniyar kasarsa na karfafa kyakkyawar dangantaka da makwabciyarsa Sudan ta kudu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China