Shugaban kwarya-kwaryan taron a wannan karo kuma shugaban kasar Vietnam Tran Dai Quang, ya bayyanawa 'yan jarida bayan rufe taron cewa, an amince da kara yin mu'amala da juna a wannan yanki, da sa kaimi ga maida yankin a matsayin muhimmin yanki na hadin gwiwar tattalin arzikin duniya, da sa kaimi ga kafa yankin ciniki cikin 'yanci a wannan yanki.
Sanarwar da aka zartas a gun taron ta ce, shugabannin kasashe membobin kungiyar APEC suna son daukar matakai masu dorewa tare, da kara inganta hadin gwiwar dake tsakanin membobin kungiyar APEC, da sa kaimi ga samun bunksuwa mai dorewa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba, da zurfafa tsarin bai daya na tattalin arziki a yankin, da nuna goyon baya ga hukumomin cinikayya da kamfanonin kanana da matsagaita, da kuma kara tabbatar da tsaron hatsi da raya aikin gona mai dorewa. (Zainab)