A jawabin da ya gabatar wa al'ummar kasar a ranar Lahadi don bikin murnar cika shekaru 57 da samun 'yancin kasar a Abuja, babban birnin kasar, shugaba Buhari ya ce, gwamnatin tarayya ta tanadi tawagar masu bincike, kuma tana tattara dukkan sahihan bayanai wadanda zasu bada damar tuhumar jami'an gwamnati da aka samu da hannu wajen aikata rashawa.
Yace dama suna tsammanin wadanda suke da hannu a aikata rashawa zasu iya daukar dukkan matakai na mayar da martani a yakin da ake da rashawar, musamman ta hanyar yin amfani da bangaren shari'a don haifar da tarnaki da kuma yin amfani da siyasa. Sai dai a cewar shugaban, gwamnatinsa ta himmatu wajen kawar da rashawa daga tsarin siyasar kasar baki daya.
Shugaban Najeriyar yace, gwamnati ta samu nasarar kwato wasu daga cikin kudaden da aka sace cikin hanzari, ya kara da cewar, Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da wasu aminan kasashen duniya game da sha'anin aikata munanan laifuka.
Buhari yace alamu sun nuna cewa ana samun karin hadin kai daga bangaren shari'ar kasar game da batun na yaki da rashawa.(Ahmad Fagam)