in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarin Mohamed Salah da ya taimakawa kungiyar Masar samun damar shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018
2017-10-19 09:26:11 cri

Kauyen Nagrig dake yankin Basioun na jihar Gharbiya, na da tazarar fiye da kilomita 150 daga arewacin birnin Alkahira, fadar mulkin kasar Masar. Wurin dake da dimbin ni'ima, da filayen da gonaki da yawa, da kuma dimbin manoma.

Duk inda a shiga a wannan karamin kauye, za a tarar da mazaunasa manya da kanana suna hirar Mohamed Salah cike da alfahari. Wannan dan kauyen na su, kuma dan wasan kwallon kafa na kungiyar Liverpool, ya taimakawa kungiyar kwallon kafar kasar samun cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a badi a kasar Rasha, bayan ya yi nasarar sanya kwallaye 2 cikin ragar kungiyar kwallon kafar Congo, a gasar neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya da suka buga a makon jiya.

Kawun Salah mai suna Zaki Abde-Fattah Ghali wanda tsohon ma'aikacin banki ne, ya shaidawa wakilinmu cewa, Salah ya kasance mai son buga kwallon kafa sosai tun yana karami. Ya ce ganin yadda yake da baiwa a wannan fanni ne ya sa babansa ya yi kokarin kula da shi, tare da tura shi kungiyoyin kwallon kafa daban daban, abin da ya sa shi zama wani tauraron dan wasa.

Ya ce kwarewar Salah ta fito ne sosai a lokacin da yake buga kwallo a wata kungiya dake birnin Masar, lamarin da ya janyo hankalin wasu kungiyoyin kasashen Turai, irinsu Basel na Switzerland da Fiorentina da Roma na Italy, sai dai a karshe ya zabi Liverpool na Birtaniya.

Yayin gasar da aka buga tsakanin Masar da Congo, a ranar 8 ga wata, Salah ya jefa kwallo cikin ragar Congo ne a minti na 63 na wasan, inda ya jefa kwallon na biyu a minti na 93 a wani bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan an yi karin lokacin wasa.

Daukacin al'ummar kasar Masar na kallon Salah a matsayin wani jarumin kasar, ganin yadda ya taimaka mata samun dama a gasa mafi muhimmanci a duniya a fannin kwallon kafa, wadda kasar ta kasa samu cikin shekaru 27 da suka wuce. Nasarar da kungiyar Masar ta samu a ranar 8 ga wata, ta sa ta zama na farko a rukuni na E, inda take gaban Uganda, Ghana da Congo.

Zaki Ghali, kawun Salah ya kara da cewa, Salah jajirtacce ne mai hazaka, kana yadda ya yi bugun daga kai sai mai tsaron ragar a gasar ya nuna haka, domin bugun ne zai iya tantance makomar gasar, tun da ba aiki ne mai sauki ba.

A nasa bangaren, Abadah Saeed Ghali, dan uwan dan Sallah ne, wanda ya girme wa dan wasan mai shekaru 25 da shekaru 10, ya ce ban da fasahar sarrafa kwallo da saurin gudu, Salah yana da da'a da mutunci. Ya ce a duk lokacin da Salah ya shiga cikin kauyen, ya kan zauna tare da daukar hoto da mutane. Haka ne kuma ya sa mutane ke kara yin alfahari da shi.

Cikin wata unguwar dake dab da gidan Salah, wani yaro mai suna Karim Saber dake tafiya sanye da wata rigar T-shirt da aka rubuta "M. Salah" a baya da lambar Salah ta kungiyarsa wato 10 a gaban rigar, ya ce yana son Salah matuka. Ya ce ya taba gamuwa da shi a cikin kauyen, har ma suka dauki hoto a dab da makarantarsa. Duk da cewa shahararren dan wasa ne, yana hulda da yara tamkar abokansa. A cewar yaron, Salah wani misali ne gare su, inda suke kokarin koyon fasaharsa yayin da suke buga kwallo.

Don nuna girmamawa ga Salah, bayan shi da abokansa sun ci nasarar akan kungiyar Congo, Gwamnan jihar Gharbiya ta canza sunan makarantar da Salah ya yi zuwa "Mohamed Salah Industrial High School". Haka zalika, ana da shirin gyara sunan cibiyar matasa ta Nagrig zuwa wani sunan da ya kunshi sunan Salah, in ji magajin Nagrig Maher Shetia. Ya ce Salah ya kafa wani asusun jin kai a cikin kauyen, kana yana da shirin kafa wata makaranta. Ban da haka kuma, ya ba da tallafi ga wani asibitin wurin wajen samar da wasu dakunan jinya, da wasu kayayyakin aiki da ake bukata.

Tsarin horar da 'yan wasan kwallon kafar matasa a kasar Masar, na mai da hankali wajen shirya gasa tsakanin makarantu. Daga bisani akan tura yaran dake da kwarewa zuwa makarantun koyon fasahar taka leda, inda za a zabi wadanda suka fi kwarewa domin su halarci jarrabawar neman zama 'yan wasa a manyan kungiyoyin kasar.

Bisa wannan tsari ne, Salah ya yi kokarin koyon fasahar buga kwallon kafa. An ce tun yana makarantar firamare, ya taimakawa kungiyar makarantarsa lashe gasar da ta gudana tsakanin dukkan makarantun jihar Gharbiya.

Reda Masoud, wani malami mai koyar da fasahohin wasan motsa jiki a Nagrig, ya ce Salah ya fara buga kwallo a kungiyar makarantar Nagrig, inda shi da abokan kungiyarsa suka lashe kambi a gasar da ake yi tsakanin makarantun jihar Gharbiya har karo 2. A cewarsa, an fara lura da dan wasan ne sakamakon kwarewarsa a fannin buga kwallo, da saurin gudu, da kuma da'ar da ya nuna.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China