in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan harbi kibiya
2017-09-28 14:51:24 cri


1) tarihin wasan harbi kibiya

Wasan harbi kibiya yana da tarihi sosai, ganin ya kasance muhimmiyar dabarar da ake amfani da ita wajen farauta, da kuma yaki a tarihin dan Adam. Sanin kowa ne kafin an samu kibiya da baka, 'yan Adam na amfani da duwatsu, da mashi ne wajen jifan dabbobi, ko kuma abokan gaba. Daga bisani aka kirkiro kibiya da baka, don maye gurbin duwatsu da mashi, ganin cewa ta amfani da kibiya, za a iya cimma wanda ake hari daga wuri mai nisa.

Yanzu haka alamar amfani da kibiya da baka mafi tarihi da aka gano a nahiyar Turai, ita ce a Stellmoor dake dab da birnin Hamburg na kasar Jamus, inda aka samu wata kibiyar da aka yi ta da ice, da dutse, a fiye da shekaru 10000 da suka wuce. A sauran kasashe an gano wasu kayayyaki masu siffar kanun kibiya, wadanda aka yi su da dutse ko kashi, sai dai yawancinsu ba a iya tabbatar da cewa ko an yi amfani da su tare da baka ne, ko kuma jifa ake yi da su ta amfani da wata fasahar ta daban. Ga misali ta amfani da na'urar jifa da mashi ko Spear-thrower a turance.

Kusan dukkan tsoffin kasashe masu tarihi, kamarsu Girka, Pasha, Indiya, Sin, Japan, da dai sauransu, sun taba kebe wasu da yawa daga cikin sojojinsu, domin su zama masu harbar kibiya. Kana mutanen Akkad, wata tsohuwar kasa da ta kasance a kudu maso gabashin kasar Iraki ta yanzu, sun fara amfani da baka da kibiya wajen yaki.

Sannu a hankali, bukatun da ake da su a fannin yaki sun sa an rika kyautata fasahar kera baka da kibiya, har ta kai an kirkiro baka irin daban daban, don dacewa da muhalli da bukatu na wurare daban daban. Ga misali, a nahiyar Turai, baka da ya fi shahara shi ne Welsh longbow, wanda yake da tsayi da girma. Yayin da a tsakiyar Asiya da nahiyar Amurka, mutane sun fi son gajeren baka, domin suna amfani da su ne a kan dawaki.

2) Tarihin harbi kibiya a Sin

Mutanen kasar Sin su ma sun dade suna amfani da baka da kibiya. An taba samun wani tsohon baka a lardin Zhejiang dake gabashin kasar, wanda aka kera shi wasu shekaru 8000 da suka wuce. Wata tatsuniyar kasar Sin ta ce, a da can akwai rana guda 10, kana wani babban gunki ya ba su umarni su rika fitowa suna nuna hasken su daya bayan daya. Amma rana ba su bi umarninsa ba, sai suka fito a lokaci guda, abin da ya sa aka yi zafi da fari mai tsanani, har ma aka fara samun gobara a wurare daban daban na duniya. Ganin haka, ya sa wani jarumi mai suna Hou Yi, wanda yake da kwarewa sosai a fannin harbin kibiya, ya yi amfani da kibiyarsa ya harbo rana daya bayan daya. Harbinsa ya sa rana guda 9 suka fada cikin teku, ban da guda daya da ta rage, wato rana da muke da ita yanzu. Wannan tatsuniya ta nuna yadda Sinawa suke martaba mutanen da suka kware a fannin harbin kibiya.

A daular Zhou ta kasar Sin, wato kimanin shekaru fiye da 3000 da suka wuce, an bukaci dattawa na lokacin da su mallaki wasu fasahohin tushe guda 6, wato sanin doka, da iya rera waka, da harbin kibiya, da tuka keken doki, da rubutu, da kuma kirga. Ka ga harbi kibiya na cikinsu. Ta haka za mu iya ganin Sinawa na lokacin, na ganin fasahar harbin kibiya da muhimmanci sosai.

Zuwa lokacin daular Han, wato kimanin shekaru 2200 da suka wuce, sojojin kasar Xiongnu, sun dinga kai hari ga daular Han, wato kasar Sin a lokacin. Mutanen Xiongnu makiyaya ne da ke da al'adar kiwon doki da kuma hawan doki. Su ma, kamar yadda muka bayyana a baya, suna da kwarewa a fannin amfani da wani irin gajeren baka, wanda ya dace da bukatar hawan doki da harbi kibiya a lokaci guda. Saboda yake-yaken da mutanen Xiongnu suke yi da mutanen daular Han, sannu a hankali, sojojin daular Han su ma suka fara amfani da irin wannan baka mai inganci. Zuwa lokacin daular Tang a tarihin kasar Sin, wato kimanin shekaru 1400 da suka wuce, sojoji suna amfani da baka iri-iri, inda masu tafiya da kafa ke amfani da baka mai tsayi, yayin da masu hawa doki ke amfani da gajeren baka, don samun saukin amfani da shi a kan doki. Sa'an nan daga daular Tang, wato kasar Sin a lokacin, fasahar kera baka da kibiya masu inganci ta yadu zuwa kasar Koriya da Japan ta lokacin.

3) Ire-iren wasanni na harbi kibiya

Bayan da aka mai da harbin kibiya ya zama wani wasan motsa jiki, an kasa shi zuwa nau'o'in wasanni iri-iri bisa dabaru daban daban da aka zaba wajen gudanar da wasan. Sa'an nan manyan wasannin harbin kibiya sun hada da Target Archery, wato wasan harbin kibiya ga abin bara. Da kuma Field Archery, wato wasan harbi kibiya a cikin daji, wanda yake tamkar kwaikwayon yadda ake farautar namun daji.

An fi gudanar da gasannin Target Archery ne karkashin jagorancin hukumar wasan harbi kibiya ta duniya WA, gasannin da suka hada da wadanda ake gudanar da su cikin dakuna, da kuma wadanda ake yi a kan wani fili dake wajen daki. Inda 'yan wasa su kan harba kibiyoyi ga abin bara, wanda ya kunshi wasu da'irori. Sa'an nan kibiyar da ta cimma karamar da'irar dake tsakiyar abin bara, za ta sanya a samu maki mafi yawa. Idan kuma kibiyar ta cimma wani gefe na abin baran, ko kuma ba ta same shi ba sam, to, makin da za a samu zai yi kadan, ko kuma zai zama sifiri.

A daya bangaren, Field Archery na bukatar a sanya wasu abubuwan bara cikin daji, sa'an nan 'yan wasa za su bi hanyar da aka shata, su tsaya a wurin da aka kayyade, su rika harba kibiya. Tsayin da ya yi kamar yadda wani mafarauci yake yawo a cikin daji, yana neman namun daji, yana harbin su.

Ban da wannan kuma akwai Clout Archery, wasan da ya shafi harba kibiya don cimma wani abu mai nisa, wanda a kan kwantar da shi a kasa. Haka kuma, akwai wasan Crossbow Archery, inda ake amfani da Crossbow, wato wata na'urar musamman irin ta hannu, wadda za ta iya taimakawa mutane harba kibiya. Ta wannan na'ura, ko da mutumin da ba shi da karfin jiki, zai iya harba kibiya zuwa wuri mai nisa matuka.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China