An tabbatar da haka ne a ranar Lahadi data gabata, yayin da aka kammala wani taro na kwanaki 3 na hukumar WBSC wanda ya gudana a Gaborone na kasar Botswana. Wannan taro shine irinsa na 2 da aka kira tun bayan da aka kafa hukumar a shekarar 2015, inda aka samu halartar tawagogi fiye da 300 da suka zo daga kasashe mambobin hukumar 130.
A lokacin da yake magana da kafofin watsa labaru a karshen taron, mista Mukokomani ya ce yadda aka kira wannan taro a karo na farko a wata kasar dake nahiyar Afirka zai taimaka wajen raya harkokin da suka shafi wasannin baseball da softball a wannan nahiyar.(Bello Wang)