in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan wasan Squash 4 za su wakilci kasar Kenya don halartar babbar gasar duniya
2017-10-19 09:28:27 cri
A ranar Asabar da ta gabata, kasar Kenya ta sanar da sunayen wasu 'yan wasa 4 da za su wakilci kasar a wajen gasar fidda gwani ta wasan Squash ta duniya karon 25, wadda za ta gudana tsakanin ranakun 27 ga watan Nuwamba zuwa ranar 3 ga watan Disamba, a Marseille na kasar Faransa.

Wasan Squash tamkar wasan tenis ne, sai dai ana yinsa ne a kan bango. 'Yan wasan 4 da za su wakilci kasar Kenya sune Chirag Shah, Bruce Jusa, James Dalidi, da Muqtadir Nimji, wadanda suka shiga jarrabawa tare da sauran kwararrun 'yan wasa 8, kafin sun ci jarrabawar a karshe.

Da ma an ba kasar Masar damar karbar bakuncin irin wannan gasar a shekarar 2015, sai dai daga bisani an dakatar da gasar sakamakon rikice-rikicen siyasa da suka abku a kasar. Don haka a wannan karo, hukuma mai kula da wasan Squash ta duniya ta zabi kasar Faransa don ta karbi bakuncin gasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China