in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun halarci bikin rufe tattaunawa tsakanin 'yan kasuwan kasashen 2
2017-11-09 15:05:30 cri

Yau Alhamis ne a nan Beijing, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin, suka halarci bikin rufe taron 'yan kasuwan kasashen 2, tare da yin jawabai.

A jawabinsa yayin bikin, shugaba Xi ya ce, bana shekara ce ta cika shekaru 45 da kasashen Sin da Amurka suka ba da "sanarwar Shanghai". A cikin shekaru 45 da suka wuce, kasashen 2 sun samu babban ci gaba ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci, wanda jama'arsu suka ci gajiya sosai. Bayanai sun cewa, akwai kyakkyawar makoma wajen inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci, kana kasashen 2 za su iya samun nasara da moriya tare.

Shugaban na kasar Sin ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ba za ta sauya manufarta ta yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje ba. Kasar Sin za ta samu bunkasuwa ne, kadai idan ta ci gaba da yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

Shugaba Xi ya kara da cewa, a matsayin Sin na kasa mai tasowa mafi girma da kuma Amurka kasa mai ci gaba a duniya, Sin da Amurkar suna iya taimakawa juna, a maimakon yin takara da juna.

A nasa jawabinsa, shugaba Trump ya ce, Amurka da Sin, abokai ne na yin hadin gwiwa, wadanda ke da dankon zumunci a tsakaninsu. Sun cimma daidaito a fannonin tattalin arziki da tsaro da dai sauransu. Habaka hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 yana taimaka musu wajen samun ci gaba. Kasar Amurka na son ci gaba da inganta hadin gwiwar moriya juna da kasar ta Sin ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci, kyautata hadin kansu ta fuskar makamashi, da kara kawo wadata a kasashen 2, da daidaita matsalolin da suke fuskanta ta fuskar tattalin arziki da kasuwanci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China