in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bayyana alakar dake tsakanin Sin da Amurka da cewa ta shiga sabon shafi a tarihi
2017-11-09 14:06:40 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka da cewa ta shiga sabon matsayi a tarihi.

Xi, ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawa tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar Sin.

Tun da yammacin ranar Laraba ne shugabannin kasashen biyu suka fara musayar ra'ayoyi game da batutuwan da suka shafi alakar dake tsakanin kasashen biyu, har ma da sauran batutuwa da suka shafi kasa da kasa domin neman cimma matsaya.

Shugaba Xi ya ce, mun yi amanna cewa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ba wai ta shafi moriyar al'ummomin kasashen biyu ba ne, har ma ta shafi zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

A cewar shugaba Xi, shi da takwaransa na Amu1rka sun amince cewar babu wani zabi da ya rage illa tabbatar da hadin kai tsakanin kasashen Sin da Amurka, kasancewar samar da kyakkyawar makoma zai tabbata ne ta hanyar hadin kai da moriyar juna.

A nasa bangaren, Trump ya bayyana cewa babu wani muhimmin batu da ya wuce tabbatar da hadin kai tsakanin kasar Sin da Amurka, ya ce kasashen biyu suna da karfin fada a ji wajen warware matsalolin duniya a cikin shekaru masu yawa dake tafe. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China