in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Amurka sun ziyarci fadar adana kayan tarihi ta Forbidden City
2017-11-08 20:42:44 cri

A yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da mai dakin sa Peng Liyuan, suka kewaya da shugaban Amurka Donald Trump da mai dakin sa Melania Trump, sassan fadar adana kayan tarihin nan mai dadadden tarihi ta Forbidden City dake nan birnin Beijing, hakan kuwa na zuwa ne a daidai gabar da shugaban na Amurka, ke ci gaba da ziyarar aiki da ya fara a nan kasar Sin a ranar farko.

A wani ci gaban kuma, shugaba Xi Jinping ya bayyana kyakkyawan fatan sa, game da nasarar ziyarar da shugaba Donald Trump ya fara gudanarwa a nan kasar Sin. Xi ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake kewayawa da Mr. Trump sassa daban daban na fadar "Forbidden City".

A wani ci gaban kuma, shugaba da mai dakin sa, tare da bakin su Donald Trump da uwar gidan sa, sun kalli wasan kwaikwayo salon birnin Beijing, wanda a turance ake kira da Peking Opera, da yammacin wannan rana, a fadar ta "Forbidden City".

Wasan kaikwayo na Pekin Opera dai na da tarhi na sama da shekaru 200, yana kuma cikin salon wasannin kwaikwayo mafiya shahara a duniya, kuma tuni hukumar UNESCO ta sanya shi cikin jerin ababen tarihi da aka gada daga kaka da kakanni.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China