in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Amurka ya ce ganawar Xi da Trump dake tafe na da ma'anar tarihi
2017-11-07 09:02:26 cri

Jakadan Amurka a kasar Sin Terry Branstad, ya bayyana ganawar da ake sa ran yi tsakanin shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na Amurka Donald Trump da cewa batu ne mai muhimmanci kuma mai ma'anar tarihi.

Branstad, ya bayyana a lokacin zantawa da 'yan jaridu a Beijing cewa, akwai abin farin ciki matuka kuma wannan ganawar ta Xi da Trump tana cike da ma'anar tarihi da muhimmanci.

Ana sa ran shugaba Donal Trump na Amurka zai kawo ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 8 zuwa 10 ga watan nan na Nuwamba, kuma wannan shi ne karo na uku da zai gana da shugaba Xi Jinping.

Ya ce, yana tunanin ganawar shugabannin biyu tana da matukar fa'ida kuma abu ne mai kyau.

Idan har shugabannin biyu suka yi aiki tare kuma suka yi kokarin kawar da dukkan banbance banbancen dake tsakaninsu, ana fata hakan zai taimakawa al'umma cimma nasarori masu yawa.

Ya kara da cewa, yin musayar ra'ayoyi tsakanin shugaba Xi da Trump zai yi matukar taimakawa wajen warware duk sabanin dake tsakanin kasashen biyu.

Babbar ajandar da ake sa ran ziyarar ta mista Trump za ta fi mayar da hankali ita ce batun takaddama kan zirin Koriya da kuma dangantakar kasuwanci tsakanin Sin da Amurka, in ji Branstad.(Ahmad fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China