Yayin bikin, Madam Prisca Mupfumira, Ministar kasar Zimbabwe mai kula da ayyukan kwadago da harkokin al'umma, ta godewa gwamnatin kasar Sin bisa tallafin da ta bayar.
A cewarta, yayin da ake raba tallafin, za a mai da hankali ga mutane masu rauni, musamman ma tsoffafi da nakasassu da marayu da mutanen da ambaliyar ruwa da sauran iftila'i suka ritsa da su
A nasa bangaren, jakadan kasar Sin dake Zimbabwe mista Huang Ping, ya ce kasarsa ta bayar da tallafin ne don cika alkawrin da shugaba Xi Jinping ya dauka yayin da ya ziyarci Zimbabwe, gami da halartar taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da ya gudana a birnin Johannesburg a karshen shekarar 2015.(Bello Wang)