in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya bukaci daliban da suka kammala karatu a cibiyar da kasar Sin ta kafa su kasance jagorori a kasashensu
2017-10-18 21:14:42 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bukaci daliban da suka kammala karatunsu a cibiyar hadin gwiwar kasashe masu tasowa da raya kasa dake fitacciyar jami'ar nan na Peking a nan kasar Sin da su kasance jagororin gyare-gyare da ci gaba a kasashensu.

Shugaba Xi ya sanar da kafa cibiyar ce yayin jerin tarukan koli da aka shirya don murnar cikar MDD shekaru 70 da kafuwa a shekara 2015. A wani mataki na horas da dalibai masu hazaka daga kasashe masu tasowa, cibiyar ta dauki jami'an gwamnati, masu tsara dokoki, da kwararru a fannin kudi da masana 48 daga kasashe masu tasowa 27 a yankunan Asiya da Afirka da Latin Amurka da Turai, a watan Satumban shekarar 2016 da ta gabata, inda za su yi karatun digiri na biyu da na uku .

A watan Yuli ne rukunin farko na dalibai 26 da suka fara karatu a wannan cibiya, suka gabatar da wata wasikar godiya ga shugaba Xi Jinping, inda suka mika godiyarsu ga kasar Sin bisa ga damar da ta ba su ta kara sanin irin nasarorin da kasar Sin ta samu a shirinta na yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

A cikin amsar da shugaba Xi Jinping ya aikewa daliban a ranar Larabar da ta gabata, shugaba Xi ya bayyana farin ciki kan yadda suka kasance daliban farko da suka kammala karatunsu a wannan cibiya.
Shugaba Xi ya ce , an kafa cibiyar ce kamar yadda daliban ke fata,don samar da daidaito, shiga a dama da su da kuma samar da ci gaba mai dorewa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China