in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya taya kungiyar kawance tsakanin Rasha da Sin murnar cika shekaru 60 da kafuwa
2017-10-10 09:58:34 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga kungiyar kawance tsakanin Rasha da Sin bisa cikarta shekaru 60 da kafuwa.

A sakon da ya aike a jiya Litinin, ya ce cikin shekaru 60 da suka gabata, kungiyar ta kiyaye ka'idojin kawance wajen kyautata huldarta da kasar Sin.

A cewar shugaba Xi, dangantaka tsakanin kasar Sin da Rasha ta kai wani sabon mataki a tarihi, yana mai bayyana fatan kungiyar za ta bude wani sabon babi na inganta musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu da ba da gagarumar gudummuwa wajen karfafa dangantaka tsakanin al'ummomin, tare da ciyar da muhimmin hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani babban mataki.

Shi ma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya aike da sakon taya murna ga kungiyar, wadda a jiya Litinin, ta shirya wata liyafa domin murnar cikarta shekaru 60 da kafuwa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China