in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A yau ne jirgin saman fasinja na farko da kasar Sin ta kera ya tashi cikin nasara
2017-05-05 15:33:57 cri

A yau Jumma'a ne jirgin saman fasinja na farko samfurin C919 da kasar Sin ta kera ta tashi cikin nasara.

Shi dai wannan jirgin saman fasinja mai injuna biyu wanda ya tashi daga filin jirgin saman kasa da kasa na Pudong dake birnin Shanghai dauke da ma'aikata 5, kadai a cikinsa, ya kuma sauka cikin nasara da misalin karfe 3:19 na yamma agogon kasar Sin.

Yanzu haka kasar Sin ta zama kasa ta hudu bayan kasar Amurka da Turai da Rasha da suka kera jiragen saman fasinja kirar Jumbo. Wannan wani babban ci gaba ne ga kamfanin kera jiragen saman fasinja na kasar Sin(COMAC) dake birnin Shanghai, kamfanin da ya kera jirgin samfurin C919.

Ma'anar harafin "C" da aka yi amfani da shi a sunan jirgin, yana nufin kasar Sin da kuma kamfanin na COMAC, yayin da lamba 9 kuma take nufin har abada a al'adan Sinanci, kana 19 tana wakiltar yawan mutane 190 da jirgin zai iya dauka.

Sabon jirgin wanda zai iya cin nisan zangon kilomita 4,075, zai iya gogayya da jirgin saman fasinja kirar Airbus 320 da kuma sabon jirgin saman Boeing 737, lamarin da ke alamta nasarar kasar Sin a kasuwarnnin jiragen sama na duniya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China