in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: Rikici da fatara ne ke kawo tsaiko ga ci gaban ilimi cikin shekaru goma da suka gabata.
2017-09-07 09:38:26 cri
Asusun kula da yara na MDD UNICEF, ya ce rikici da fatara sun kawo tsaiko ga ci gaban ilimi cikin sama da shekaru goma da suka shude a fadin duniya.

UNICEF ya ce yara a kasashen da suka fi fama da talauci da yankunan dake rikici, su ne matsalar ta fi shafa.

Ya ce daga cikin yara miliyan 123 da ba sa zuwa makaranta, kashi 40 na na rayuwa ne a kasashen dake da karancin ci gaba, yayin da kashi 20 ke yankunan dake fama da rikici.

Rikice-rikice a Iraqi da Syria sun kara adadin da miliyan 3.4, abun da ya kawo adadin yara da ba sa zuwa makaranta a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afrika zuwa kusan miliyan 16.

A cewar UNICEF, la'akari da matsananciyar fatara da karuwar adadin al'umma da aukuwar bukatun gaggawa a yankin sahara na Afrika da kudancin Asia, yawan yaran da ba sa makarantar firamare da karamar Sakandare ya mamamye kashi 75 cikin dari na adadin a duniya.

Daga cikin kasashen da suka fi fama da talauci, kasashen Habasha da Niger sun fi samun nasara, inda adadin yaran da suka shiga makaranta ya karu da kashi 15 a Habasha yayin da ya karu da kashi 19 a Nijer.

A daya bangaren kuma, karancin kudaden tallafawa bangaren ilimi na mummunan ya kawo tasiri ga yunkurin sanya yara makaranta a yankunan dake fama da rikici. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China