in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoton MDD: Yara miliyan 600 za su fuskanci karancin ruwa nan da shekarar 2040
2017-03-23 13:49:48 cri
Asusun yara na MDD ya ce, ya zuwa shekarar 2040, kimanin kashi daya daga cikin hudu na yaran duniya wadanda za su kai miliyan 600 za su fuskanci karancin ruwa a shiyyar da suke da zama.

Asusun ya fadi hakan ne a wani rahoton da ya fitar a jiya Laraba 22 ga wata, ranar da ta kasance ranar ruwa ta duniya.

Rahoton mai taken "ruwa da yara da ke fuskantar sauye-sauyen yanayi", ya yi nazari a kan barazanar da yara kan iya fuskanta sakamakon karancin ruwa da kuma yadda sauye-sauyen yanayi za su tsananta barazanar.

Rahoton ya kuma gabatar da jerin shawarwari dangane da yadda za a saukaka tasirin da sauye-sauyen ke haifarwa ga albarkatun ruwa, ciki har da tsara shirye-shirye game da albarkatun ruwa daga bangaren gwamnati, da kuma bai wa yaran da ke fama da matsalar fifikon karancin sa damar samun ruwa mai tsafta.

Har wa yau, ya dace a yi la'akari da sauye-sauyen yanayi, a yayin da ake tsara manufofin da suka shafi ruwa da kiwon lafiya da dai sauransu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China